23 Agusta 2017 - 19:57
Harin Kunan Bakin Wake Ya Lashe Rayukan Mutane Akalla 4 A Kasar Kamaru

Wani karamin yaro da aka masa jigida da bama-bamai ya tarwatse a tsakanin jama'a a yankin arewacin kasar Kamaru, inda ya janyo mutuwar mutane akalla 4 yammacin jiya Talata.

Majiyar 'yan kato da gora da suke taimakawa jami'an tsaron kasar Kamaru a fagen yaki da 'yan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram ta sanar da cewa: Wani karamin yaro da 'yan kungiyar Boko Haram suka masa jigida da bama-bamai ya tarwatse a tsakanin jama'a a kauyen Amchide da ke yankin arewacin kasar kusa da kan iyaka da kasar Nigeriya, inda ya kashe mutane biyu nan take, sannan bayan kai wadanda suka samu raunuka asibiti, aka kara samun karin mutuwar wasu mutanen biyu na daban. 

Wata majiya ta bayyana cewa karamin yaron ya tarwatse ne a tsakanin tawagar 'yan kato da gora da suke tallafawa jami'an tsaron Kamaru a fagen yaki da ta'addancin kungiyar Boko Haram, kuma hare-haren kungiyar ta Boko Haram sun fi kamari ne a yankin arewacin kasar ta Kamaru kusa da kan iyaka da tarayyar Nigeriya, inda ko a ranar 5 ga wannan wata na Agusta harin kunan bakin waken ya lashe rayukan mutane 8 a kauyen  Ouro-Kessoum a arewacin kasar ta Kamaru.288